Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Gwamnan Kaduna: Uba Sani Ya Fi Kowa Cancanta – Jama’ar Kudan

Al’ummar karamar hukumar kudan dake jihar Kaduna, sun bayyana Sanata Uba Sani a matsayin Dan takarar da yafi Kowane Dan takarar cancantar zama gwamna jihar Kaduna.

Bayanin haka ya fito ne daga shugaban karamar hukumar kudan Honarable Shu’aibu Bawa Jaja, a yayin da yake jawabi a dandamalin taron magoya bayan jam’iyyar APC da suka tarbi Sanata Uba Sani a filin wasa na kudan.

Bawa Jaja ya ce, idan za’a yi maganar kwarewa da cancanta ne, to kaf babu tamkar Uba Sani, domin shi yayi angani a kasa, ba kamar sauran yan takarar ba, wanda basu taba tsinanama Al’ummar su komai ba.

Shu’aibu Jaja ya bayyana cewa, su ilahirin Al’ummar karamar hukumar kudan Uba Sani zasu zaba daga sama har kasa, domin shine zabin Al’ummar jihar Kaduna.

Shima a nasa jawabin, Dan takarar zama gwamnan jihar Kaduna a jam’iyyar APC, Sanata Uba Sani ya bayyana cewa lallai zai inganta rayuwar mata da mata sa da kuma dukkan al’ummar jihar Kaduna in har ya samu damar zama gwamna a jihar Kaduna.

Sanata Uba Sani ya ce, “Hakaki ingatanta rayuwar matasa da mata da sana’o’i da ilimi shi ne abu mafi kyau ga al’ummar jihar Kaduna.”

Sanatan ya ci-gaba da cewa, “Idan har Allah ya ba shi dama, zai yi iyakacin bakin kokarin sa don ganin ya habaka harkar ilimi, tsaro, lafiya, ruwan sha, wutan kantarki da sauran abubuwan more rayuwa ga dukkan al’ummar jihar Kaduna.”

Haka kuma Sanata Uba Sani ya nuna bakin cikin sa a kan yadda daliban sakandare da ke Kudan ba su rubuta jarabawar kammala sakandare (WAEC), sai sun je Zariya. Inda ya ce, “Lallai in dai ya zama gwamna dukkan waɗannan abubuwa sun kau.”

Wani abin mamaki, duk da cewa garin Kudan mahaifar dan takarar zama gwamna ne na jam’iyyar adawa PDP, amma jama’ar Kudan sun ba wa maras da kunya, domin kuwa sun nuna lallai Sanata Uba Sani shine zabinsu.

A yayin ziyarar, Sanata Uba Sani, ya kaddamar da ginin katafaren dakin kwafuta ICT centre a government secondary school hunkuyi, wanda zai gina a karamar hukumar kudan kamar yadda ya gina a sauran kananan hukumomin jihar Kaduna.

Sannan ya roke su da su fito ranar zabe, su zabi jam’iyyar APC daga sama har kasa a ranar zaben shugaban kasa, yan majalisa da kuma na gwamnoni.

Exit mobile version