Gwamnan Binuwai Ya Zargi Buhari Da Marawa ‘Yan Bindigar Fulani Baya

Gwamnan jihar Binuwai Samuel Ortom, ya zargi Shugaban kasa Muhammadu Buhari da yi wa ‘yan Bindigar Fulani sharen fage domin su mamaye Nijeriya da mayar da ‘yan ƙasa bayi a kasar su.

Ortom ya bayyana hakan ne yayin jawabin da ya yi a ranar Talata kan kisan da ake zargin makiyaya fulani ne suka yi a sassan yankin Arewa ta Tsakiya.

Ortom ya kuma koka kan cewa a kalla mutane 70 ne aka kashe cikin makwanni biyu da suka gabata a kananan hukumomi uku a jihar, inda ya ce ba zai yi wu a cigaba da tafiya a hakan ba.

“Menene ke faruwa yanzu, ni dai, abin a fili ya ke, Shugaban kasa yana yi wa Fulani aiki ne domin su karbe kasar baki daya.” Ya cigaba da cewa alama da ya ke gani daga Shugaban kasar ta rashin daukan matakan da suka dace ya nuna cewa shi shugaba ne kawai na Fulani duk da ya dade da sanin haka.

“Muna sauyawa zuwa kasa mara doka, idan muna da shugaban kasa da ya bawa jami’an tsaro umurnin su harbe duk wanda suka gani da AK-47 sannan ministan tsaro ya fito ya ce ba za su iya harbi hakan nan ba … toh, wanene kwamandan rundunar sojoji na kasar?,” in ji Ortom.

Labarai Makamanta

Leave a Reply