Gudun Sharholiya Ya Sa Ni Barin Amurka Ranar Bikin Haihuwata – Buhari

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya ce ma’aikatan fadarsa sun hana shi cika burinsa na yin bikin ranar zagayowar haihuwarsa salim -alim.

Buhari ya ce dalilin ke nan ma da ya sa da gangan ya sanya ranar dawowarsa daga Amurka ta kasance a ranar bikin.

Ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi ga Shugaban Ma’aikatan Fadarsa, Farfesa Ibrahim Gambari da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da ma wasu daga cikin ma’aikatan fadar shugaban da suka taru don taya shi murna ranar Litinin.

Shugaban ya nuna godiyarsa da dimbin katinan taya shi murna da sakonnin fatan alheri kan cikarsa shekara 80 a duniya da ya yi ranar Lahadi.

Sai dai Buhari ya ce a wajensa, ranar ba ta da wani bambanci da sauran ranakun aiki.

A sakon da Farfesa Gambari ya karanta a madadin ragowar ma’aikatan Fadar Shugaban Kasar, ya ce, “Muna alfahari da kai ya mai girma Shugaban Kasa saboda damar da ka ba mu ta hidimta wa Najeriya cikin girmamawa.”

Labarai Makamanta