Gudu Daga Filin Yaƙi: Rundunar Soji Ta Kori Jami’anta 300

Hukumar sojin Nijeriya ta sallami sama da jami’ai 300 kan laifin guduwa daga filin yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram na rundunar Operation Lafiya Dole a Arewa maso gabashin Nigeria.

Kwamandojin rundunar ne suka sallami Sojin tsakanin 2015 da 2016, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Binciken ya kara da cewa bayan masu laifin arcewa daga faggen fama, an sallami wasu kan laifin amfani da kwalin karatun boge, lambar BVN na bogi, da wasu laifuffuka.

An sallami Sojojin 118 tAsk Force Bataliya, Kaura Cross, Bada a ranar 13 ga Disamba 2015, kan laifin kin shiga motar yaki daga Maimalari zuwa Baga.

Sojojin sun yi korafi kan motar kuma saboda haka suka kwashe kwanaki biyar suna tattaki zuwa faggen fama a Baga domin kwaceta daga hannun Boko Haram.

Yayin da suka isa Baga, kwamandansu, Kanal S. Omolori, ya tuhumesu da laifin arcewa kuma ya sallami 24 cikinsu.

Makonni uku bayan haka a ranar 4 ga Junairu, 2016, Omolori ya sake sallaman karin Sojoji 30 kan zargin laifin guduwa da faggen fama.

Hukumar Sojin Najeriya ta sallami jami’ai 300 kan laifin guduwa daga faggen yakin Boko Haram.

Bincike ya nuna cewa na sallami Sojojin 157 Bataliya 45 ranar 16 ga Junairu, 2016 kan laifin tafiya hutu ba tare da izini ba.

Hakazalika ranar 28 ga Febrairu, 2016, an sallami sojoji 24 kan laifin zuwa hutu ba tare da izini ba yayinda aka sallami sabbin Sojoji 36 daga Depot kan laifin amfani da kwalayen bogi, matsalar BVN, da sauransu.

Bincike ya nuna cewa wasu sojojin da aka sallama sun kalubalanci hakan inda suka zargi kwamandojinsu da zalunci.

Tsaffin sojojin suna kira ga babban hafsan sojin Nijeriya, Laftanan Janar Tukur Buratai, kan a dawo da su gidan Soja.

Labarai Makamanta