Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar kwana guda bayan da aka yi jana’aizar tulin mutanen da aka kashe a Mallagum-Kagoro a karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna, ‘yan bindiga sun sake kai wani mummunan hari a daren Juma’a 24 ga watan Disamba.
Harin yazo kwanaki biyu kafin bikin Kirsimeti ya faru ne tsakanin karfe 9:00 zuwa 9:45 na dare yayin da ‘yan bindigan suka yi yi ta harbe-harben kan mai uwa da wabi.
Wani mazaunin yankin da ya zanta da jaridar Daily Trust ya shaida cewa, ‘yan bindigan sun zo ne da manyan makamai, kuma suka yi harbi kan mai uwa da wabi akan mazauna kauye. Sai dai an yi nasarar dakile harin, domin kuwa, sojoji sun zo cikin gaggawa tare da fatattakar ‘yan ta’addan.
Sai dai, ya zuwa yanzu dai ba a sami cikakken bayani a hukumance ba daga hukumomin gwamnati. Hakazalika, majiya ta kira kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Kaduna, Muhammad Jalige, amma bai amsa waya ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
You must log in to post a comment.