Goron Karshen Shekara: El Rufa’i Ya Gwangwaje Ma’aikata


Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Ma’aikatan Jihar za su samu ƙarin albashi na wata ɗaya, kamar yadda gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai ya bayyana a cikin wata sanarwa.

Kananan ma’aikata za su samu ƙarin kusan kashi 100 na albashinsu, yayin da manyan ma’aikata kuma za su samu kashi 30 a matsayin garaɓasar ƙarshen shekara.

Ma’aikatan da ke matakin aiki daga 1-7, gwamnatin Kaduna ta ce za su ƙarbi albashin wata biyu, wato kashi 100 na albashin da suka saba karɓa.

Ma’aikatan da ke matakin aiki daga 8 zuwa 13, za su samu kashi 40 na albashinsu, yayin da kuma manyan ma’aikata daga matakin aiki na 14 zuwa sama za su samu ƙarin kashi 40 na albashinsu.

Gwamnatin Kaduna ta ce naria biliyan 1.382 za ta kashe na kuɗin garabasar ta ƙarshen shekara da ta za ta ba ma’aikata.

Labarai Makamanta