Rahotanni daga jihar Gombe na nuna cewa sama da kashi 80 cikin 100 na shugabannin APC daga karamar hukumar Yamaltu/Deba sun yi murabus daga mukamansu sakamakon takaddamar da ta barke tsakanin Sanata Danjuma Goje da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya a kwanakin baya.
Shugabannin sun sanar da matakin ne a ranar Alhamis, 25 ga watan Nuwamba bayan taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da suka gudanar a Gombe babban birnin Jihar.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan kammala taron, tsohon shugaban jamâiyyar APC na karamar hukumar, Alhaji Sulaiman Ibrahim, ya ce shugabannin unguwannin sun yi murabus daga ofisoshinsu ne saboda rashin mutunta Sanata Goje da aka yi.
Hakazalika, ya ce kai wa ayarin motocin Sanata Goje hari, makwanni uku da suka gabata na daga cikin dalilin yin murabus dinsu, domin hakan na nuna cewa da matsala a shugabancin Jihar.
Ya ce shugabannin jamâiyyar APC sun cimma matsayar ne bayan taron masu ruwa da tsaki na jamâiyyar daga karamar hukumar. Shugabannin sun yi Allah-wadai da harin da aka kai wa Goje, inda suka ce suna bayan Sanatan bisa laâakari da irin rawar da ya taka wajen ci gaban jihar Gombe da kasa baki daya.
Ya kara da cewa, ga âyaâyan jamâiyyar da ke jihar, Sanata Goje shi ne daya tilo shugaban jam’iyyar da aka amince da shi, kuma ya cancanci a girmama shi sosai idan aka yi laâakari da irin rawar da ya taka wajen kafa jamâiyyar da kuma raya ta.
âA gaskiya ma, babbar rawar da ya taka ne ta kai ga fitowar Muhammad Inuwa Yahaya a matsayin gwamnan jihar da kuma nasarar da jamâiyyar ta samu a dukkan matakai.
âSaboda haka, a matsayinmu na shugabannin siyasa na APC a unguwanni 11 na karamar hukumar Yamaltu/Deba. Don haka muna tabbatar da goyon bayanmu da biyayyarmu ga Sanata Goje a matsayin fitaccen shugaban jamâiyyar APC a jihar Gombe na gaskiya.
You must log in to post a comment.