Gombe: Mutane Da Dama Sun Mutu Dalilin Ziyarar Sanata Goje

Rahotanni daga garin Gombe fadar Gwamnatin Jihar Gombe na bayyana cewar mutane da dama sun mutu dalilin tarzomar da ta tashi bayan shigar tsohon Gwamnan Jihar Sanata Ɗanjuma Goje garin a ranar Juma’a.

Gwamnatin Jihar ta yi Allah-wadai da hatsaniyar da ta faru a babban birnin jihar, yayin da ziyarar da tsohon gwamnan jihar kuma Sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya Sanata Danjuma Goje ya kai.

Cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na Jihar Julius Ishaya Lepes ya fitar ya ce Goje ya tattaro ‘yan daba daga kananan hukumomin jihar daban-daban dauke da makamai domin su raka shi inda zai je daga filin jirgin saman da ya sauka.

Sanarwar ta kara da cewa ko a bara lokacin babbar sallah yaran Sanata Goje sun tayar da hayaniyar da kuma ta yi sanadin mutuwar mutum biyu a lokacin.

Sai dai Sanata Goje shi ma ya fitar da sanarwa kan lamarin inda yake cewa gwamnati ta aike masa da ‘yansanda su ka tare masa hanya da kuma kai hari kan jerin gwanon motocinsa, lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa daurin auren jikarsa.

Sanarwar da mataimakiyarsa ta musamman kan harkokin yada labarai Lilian Nworie, ta fitar ta ce mutam daya ya mutu yayin wannan hatsaniya, abin da bai yi wa Sanata Goje dadi ba.

Amma gwamnatin jihar ta ce mutum biyar ne suka mutu a bayanan da ta samu ya zuwa yanzu.

An kama direban Goje Aminu Hula da kuma shugaban matasan APC Kawu Lero na jihar Gombe, in ji sanarwar da Lilian ta fito.

Labarai Makamanta