Gombe: Gwamnati Ta Share Wa Al’ummar Herwagana Hawaye

Al’ummar Unguwar Herwagana dake garin Gombe sun cika da murna tare da bayyana farin cikin su bisa kawo musu dauki da gwamnatin jihar tayi wurin gyara musu kwari da ya dade yana addabar su, wanda yake silar janyo rushewar gidaje.

A wata ziyarar gani da ido da gwamnan jihar Muhammad Inuwa Yahaya ya kai inda ake gudanar da aikin ya bayyana jin dadi da yadda yaga aikin ke gudana,yana mai cewa aikin wani kokari ne na gwamnatin shi wurin kyautata rayuwar al-umma.

Hakanan gwamnan ya kuma duba aiki hanya da gwamnatin keyi a unguwar idi da unguwa uku da Kagarawal da kuma Malam Inna mai tsawon kilomita hudu da rabi,inda ya bayyana jin dadi da yadda aikin ke gudana.

Gwamnan ya ja hankalin al’ummar Unguwannin da cewa su guji yin gine-gine a filaye da tuni aka biya su diyya saboda ana barin irin filayen ne a gefen hanyar domin samar da ruwan sha da sauran ababen more rayuwa kamar wutar lantarki da sauran su.

Ya ja hankalin al’umma da su rungumi dabi’ar kulawa da ababen more rayuwa da ayyukan cigaba da gwamnati ke samar musu domin samun cigaba mai dorewa.

Labarai Makamanta