Gombe: Gwamna Inuwa Ya Kaddamar Da Rabon Tallafin Kayan Abinci

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da manufofin da za su bai wa ‘yan asalin jihar damar samun kyakkyawan shugabanci ta hanyar samar da shirye-shirye da zasu tallafawa rayuwa musamman a lokutan da ake da bukata.

Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana hakan ne a wajen bikin kaddamar da kayan tallafi ga mabukata masu kananan karfi karo na biyu a karamar hukumar Dukku dake jihar.

Gwamna Inuwa ya ce rabon kayayyakin agajin tamkar al’adar gwamnatinsa ce na nufin magance wahalhalun da mutane suka fuskanta a lokacin da ake fama da annobar Korona da kuma mutanen da bala’in ambaliyar ruwa ya shafa da kuma sama da 2000 wadanda rikicin Billiri ya shafa.

Ya ce Gwamnatin Jiha a karkashin jagorancinsa tun a baya ta kaddamar da shirin raba kayan agaji a duk fadin jihar, ta kashe zunzurutun kudi har Naira miliyan 775 kan kayayyakin agaji ga jama’ar jihar don magance matsalolin da suke fuskanta.

A jawabin sa Gwamna Inuwa Yahaya ya sake nanata kudirin gwamnatinsa na inganta walwala da jin dadin al’ummar jihar, ya ce Gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki da dukiyar dake akwai don magance bukatu da damuwar mutanen da ya rantse cewa zai shugabanta ba tare da la’akari da banbancin Kabila, addini ko siyasa ba.

Inuwa ya bayyana cewa a shekarar da ta gabata 2020, gwamnatinsa ta sami damar tallafawa sama da gidaje dubu 65 na marasa karfi inda akalla mutane 6 a kowane gida sukaci gajiyar shirin, ya kara da cewa a wannan karo ma za a cimma wannan adadi.

Gwamna inuwa yace “Gwamnatina ta talakawa ce kuma muna nan muna aiki don inganta rayuwarsu. Za mu fito da tsare-tsare masu kyau da za su iya bunkasa tattalin arzikinsu ta yadda za su iya taimakawa gwamnati da ma wadanda ke ci gaba da gwagwarmayar rayuwa”.

Dangane da wasu bukatun da Shugaban karamar Hukumar Dukku ya gabatar, Gwamna Inuwa ya ce gwamnatinsa ba ta yi watsi da matsalar karancin ruwa ba a yankin, saboda haka ne ma gwamnati ta hada gwiwa da shirin gwamnatin tarayya na PWASH da kuma farfado da hukumar RUWASSA da gwamnatinsa ta yi don magance kalubalen ruwa a kananan hukumomin Dukku, Kwami, Furnakaye da Balanga, ta yin la’akari da sune yankunan da suke kan gaba wajen fama da matsalolin ruwan sha a jihar.

Gwamnan ya bayyana cewa tare da wadannan ayyukan da gwamnatinsa ke yi, kalubalen karancin ruwa kan iya zama tarihi nan ba da jimawa ba a cikin kananan hukumomin.

Kazalika Gwamnan ya tabbatar wa mutanen karamar hukumar Dukku aniyar gwamnatin sa na kammala Gandun kiwo na Wawa-Zange domin amfanin jama’ar jihar, yana mai cewa za a shimfida hanya da za ta hade garin Gombe Abba da karamar hukumar Alkaleri na jihar Bauchi domin samarda saukin zirga-zirga.

“Bari na tabbatar wa mutanen Gombe cewa Gwamnatin Jiha a karkashin jagoranci na za ta tabbatar da cewa kowace yanki ta samu hanya, makarantu, ruwa da wuraren kiwon lafiya. Abin da kawai muke bukata daga gareku shi ne hadin kai da fahimta” inji Gwamna Inuwa.

Tun da farko da yake jawabi shugaban Kwamitin Raba kayan wanda shine mukaddashin gwamnan Jihar Gombe, Dokta Manassah Daniel Jatau ya ce don tabbatar da daidaito, a cikin aikin, Gwamnatin Jiha karkashin jagorancin Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ta kafa kwamitinsa wanda aikin komitin yanzu ya mamaye yankunan jihar, unguwanni har zuwa rumfunan zabe.

Manasa yace, kwamitin yana aiki don tabbatar da cewar kayan agajin sun isa ga mutanen da akayi domin su.

Ya ce wadanda za su ci gajiyar zasu tafi gida da kilo 10 na shinkafa, kilo 2 na sukari da kuma katan guda daya na indomie ko kuma spaghetti, yana mai cewa wannan shine za a bai wa duk wadanda suka ci gajiyar a duk fadin jihar.

Shugaban karamar hukumar Dukku, Jamilu Ahmed Shabewa ya yaba wa Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ba don kawai ya zabi Dukku ba, sai don tausayinsa ga talakawa da marasa karfi a cikin al’umma da kuma son sake sanya jihar ta zama fitila a arewa maso gabas.

Mai martaba Sarkin Dukku, Alhaji Haruna Abdulkadir Rashid II, ya ce kaddamar da fara aikin raba kayan tallafin ba wai kawai an fara a kan lokaci ba ne, alama ce da ke nuna cewa Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya jagora ne dake mutunta bukatar alumma a zuciyar sa.

Mai martaba Sarkin Dukku, ya yi kira ga mutane da kada su gajiya wajen tallafawa manufofi da shirye-shirye na gwamnatin Inuwa Yahaya don ci gaban Karamar Hukumar Dukku da kuma jihar baki daya.

Wannan jawabi yana kunshe ne cikin sanarwar da Daraktan yada labaru na gwamnan jihar Gombe Ismaila Uba Misilli ya fitar.

Labarai Makamanta