Gombe: Gwamna Inuwa Ya Bukaci A Kwashe Tubabbun Boko Haram Daga Jihar

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya ce ‘yan Boko Haram da ke sansanin gyaran hali na ‘yan Boko Haram da ke Kwami ta jihar Gombe ya kamata a mayar dasu jami’ar soji da ke Biu a jihar Borno.

Yahaya ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar babban kwamandan runduna ta 3 da aka fi sani da Operation Safe Haven, Manjo Janar Ibrahim Ali, a gidan gwamnati ranar Talata.

Ya ce duk da samar da matsuguni ga shirin na Gwamnatin Tarayya, sansanin ya karbi bakuncin wadanda ba ‘yan asalin jihar ba, ya kara da cewa bai kamata a sanya jihar ta sha wahala wajen daukar irin wannan lamari ba.

Sansanin wanda ya gyara daruruwan tubabbun ’yan Boko Haram daga sassan Arewa-maso-Gabas, wuri ne da gwamnatin jihar ta gina wa masu yi wa kasa hidima a matsayin sansani.

“Gombe ta kwashe shekaru shida tana karbar bakuncin gyaran ‘yan ta’adda.” Yahaya ya bayyana cewa, a farko an tsara shirin karbar bakuncin ne na watanni shida, amma ya lura cewa, batun ya so sauyawa zuwa na dindindin. Ganin haka, gwamnan ya ce gwamnatin Gombe ba za ta iya ci gaba da lura da wannan aikin ba.

A cewarsa, kasancewarsu a jihar Gombe ya jefa jihar cikin wahalhalu da suka shafi noma da sauran lamurran yau da kullum.

Labarai Makamanta