Gombe: An Yi Tir Da Sake Bayyanar ‘Yan Kalare

Al-ummar jihar Gombe na cigaba da yin Allah wadai da tofin Allah ya tsine akan sake bullowar aika-aikan matasa ‘yan bangar siyasa da akafi Sani da ‘yan kalare a jihar.

Idan dai za a iya tunawa kwanan nan ‘yan kalare a Gombe sun sake dawo da mummunar aika-aikan su na fadace_fadace dake kai wa ga asarar rayuka da dukiyoyi, don ko a kwanan nan ‘yan kalare sun kashe mutum uku a unguwar Jeka da fari baya ga wani jami’in soja da suka kashe a unguwar Dawaki duk a cikin garin Gombe.

Da suke caccakan lamarin na ‘yan Kalare Ibrahim Yusuf Shugaban kungiyoyin fararen hula na jihar Gombe da Alhaji Saidu Sulaiman mai kusa wani Shugaban al’umma a Gombe sun yi kira ga gwamnatin jihar da Jami an tsaro su dauki mataki irin na ba sani ba sabo akan matasa ‘yan kalaren dake jefa tsoro a zukatan jama’a, suna masu karawa da cewa daukar matakai masu tsauri za su taimaka matuka wurin magance matsalar ta ‘yan kalare.

Anasu bangarorin rundunar ‘Yan sanda ta jihar Gombe da rundunar tsaro ta farar hula wato Civil defence sun ce tuni sun gano wurare wato maɓoyar ‘yan kalaren harma sun tsare wasu ‘yan kalaren, a kokarin magance matsalar tasu.

Labarai Makamanta