Gobarar Sokoto: Gwamnatin Zamfara Za Ta Bada Tallafin Miliyan 50

Gwamnatin Zamfara za ta bayar da tallafi kudi naira miliyan 50 Ga ƴan kasuwar Sokoton wanda iftila’in gobara babbar kasuwa ya shafa da kwanakin baya.

Kamar yanda jaridar Channels ta ruwaito, sanarwa ta fito daga bakin mai baiwa Gwamnan shawara na musamman kan wayar da kai da kuma harkar sadarwar wato Zailani Baffa yayin ziyarar jajantawa da ya wakilci gwamnatin ta Zamfara a gidan Gwamnatin Sokoto.

“Abinda ya shafi Sokoto tabbas mu ma Zamfara ya shafe mu saboda dole mu yi kokarin mu bada gudummawar mu”, inji Gwamna Matawalle.

Sannan ya bada uzurin abinda ya hana su zuwa jaje da wuri wanda ya bayyana bai wuce matsalar tsaron da jahar ta Zamfara ke fama dashi, inda ya karkare da neman taimako na Addu’ar sokotowa kan lamarin.

Labarai Makamanta