Gobarar Katsina: Ganduje Ya Ba ‘Yan Kasuwa Gudummuwar Miliyan 20

Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya Jagoranci tawagar Gwamnati zuwa Jiha Katsina domin jajantawa Gwamnatin Jihar Katsina da ‘yan kasuwa da suka gamu da iftila’in gobara tare da basu tallafin kudi naira milyan 20 don rage radadin asarar da suka yi

Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari shine ya karbi tawagar, sannan ya karbi gudummawar a madadin ‘yan kasuwar, inda ya godewa Takwaransa na Jihar Kano bisa wannan namijin kokari da ya yi, su ma ‘yan kasuwar da abin ya shafa sun yi godiya ga Gwamnatin Jihar Kano.

Daga bisani aka yi addu’ar Allah ya kiyaye afkuwar haka a gaba.

Labarai Makamanta