Gobara Ta Sake Ta’adi A Majalisar Dokokin Jihar Katsina

Labarin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewar wata Gobara ta kone wani sashin zauren majalisar dokokin jihar watanni takwas bayan zauren ya yi fama da matsala makamanciyar wannan.

Kakakin majalisar dokokin jihar ta Katsina Honorabul Tasi’u Maigari, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin, yace wutar ta yi barnan ne ranar Lahadi da daddare.

Kakakin majalisar yace wutar ta taba ofishin magatakardan majalisa, mataimakinsa da kuma dakin ‘yan majalisu.

Labarai Makamanta