Gobara Daga Kogi: Sabon Rikicin APC Na Neman Cinye Kujerar Mai Mala Buni

Labarin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC sun bukaci kwamitin rikon kwarya karkashin jagorancin gwamna Mai Mala Buni, ya aje aikinsa ko su yi fatali da shi.

Da yake jawabi ga manema labarai ranar Alhamis a Abuja, kakakin kwamitin masu ruwa da tsaki, Mista Ayo Oyalowo, yace kwamitin Buni ya gaza shawo kan rikicin da yaƙi ci yaƙi cinyewa a APC.

Ya kuma yi zargin cewa kwamitin ba shi da wani shiri na shirya babban gangamin taron jam’iyyar APC na ƙasa nan kusa, lamarin dake ƙara jefa ruɗani cikin jam’iyyar.

Hakanan kuma ya kira tarukan APC a matakin gundumomi, ƙananan hukumomi da jihohi a matsayin mafi muni a tarihin jam’iyyar kuma babban abin kunya ga shugabancin Mai Mala Buni.

Mista Oyalowo yace tarukan da Kwamitin ya gudanar, maimakon ya kara wa jam’iyyar ƙarfi, sai ya koma yana raba kan mambobin jam’iyya. Dalilin da yasa APC ta sha ƙasa a zaɓen Jihar Anambra kenan inji shi.

“Gazawar kwamitin Buni ne ya jawo rashin nasarar jam’iyyar APC a zaɓen gwamnan Anambra na ranar 6 ga watan Nuwamba. Kuma an samu matsala ne tun a zaɓen fidda gwani.”

Ya ƙara da cewa tun farko sun tura sako ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, mataimakinsa, Yemi Osinbajo, jagoran APC Bola Tinubu, Sanata Ahmad Lawan da Kakakin majalisa Femi Gbajabiamila, domin su shiga ciki.

Oyalowo, wanda ya wakilci wasu mambobin kwamitinsu, ya kuma nuna goyon bayansa kan tsarin fitar da ɗan takara kai tsaye a zaɓen ƙasar nan. “Sanannen abu ne ga dukkan mambobin APC maza da mata cewa kwamitin rikon kwarya ba zai iya shawo kan matsalolin da ake fama da su ba.” “Kwamitin ya haifar da wasu matsalolin maimakon ya warware waɗanda ya samu a jam’iyya.”

Labarai Makamanta