Giwar Afirka: Najeriya Za Ta Tallafawa Chadi Da Wutar Lantarki

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ta fara shirin bai wa kasar Chadi da ke da makwabtaka da Najeriya wutar lantarki. Idan za mu tuna, gwamnatin kasar Chadi ta roki a farfado da tattaunawar da aka fara kan cewa Najeriya za ta fara bata wutar lantarki.

Jakadan kasar Cahdi a Najeriya, Abakar Saleh Chahaini ne ya mika wannan kokon barar a yayin ziyarar da ya kai wa ministan wutar lantarki na Najeriya a Abuja, Injiniya Abubakar Aliyu.

Abakar Saleh Chahaimi ya sanar da cewa, a lokutan da suka shude, kasashen biyu sun fara kulla yadda Najeriya za ta dinga bai wa Chadi wutar lantarki amma ba a kai ga kulla yarjejeniyar ba.

Saboda hakan ne ya sake mika kokon bararsa gaban ministan domin ya tabbatar da cewa kasashen biyu za su yi amfani da shirin, kamar yadda aka tsara.

A cewar Jakadan, bayan yarjejeniyar da bankin duniya ya dauka dawainiya ta kawo wuta daga kasar Kamaru zuwa Chadi, za a samu karin hadin kai babu shakka.

A bangaren ministan wutar lantarkin Najeriya, Injiniya Abubakar Aliyu, ya bai wa Chahaimin tabbacin cewa za a cigaba da maganar samar da wutar lantarkin. Ya ce daraktocin ma’aikatar wutar lantarki da ke da masaniya kan inda aka tsaya a batun, za su cigaba da duba lamarin.

Labarai Makamanta