Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jam’iyyar APC mai mulki a ta gayyaci zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, tare da mataimakinsa Kashim Shettima, da sauran zaɓaɓɓun sanatoci na ‘yan majalisar wakilai na jam’iyyar zuwa wata ganawa ta musamman.
An tsara gudanar da ganawar ranar Litinin a fadar gwamnati da ke Abuja babban birnin ƙasar.
Rahotonni na cewa an tsara ganawar ne domin tattauna batun shugabancin majalisun dokokin ƙasar biyu da yadda za a rarraba muƙaman majalisun zuwa shiyyoyin ƙasar daban-daban.
Gayyatar ganawa da zaɓaɓɓun wakilan – wadda sakataren jam’iyyar na ƙasa, Iyiola Omisore ya sanya wa hannu aka kuma wallafa a shafin jam’iyyar na Twitter – ta bayyan cewa za a yi ganawar ne ranar Litinin 13 ga watan Maris da misalin ƙarfe 12:00 na rana.
Jam’iyyar ta kuma buƙaci duka zaɓaɓɓun wakilan su hallara tare da takardun shaidar cin zaɓe da hukumar zaɓen ƙasar ta ba su.
Ganawar na zuwa ne bayan da tuni wasu ‘yan majalisun suka fara bayyana sha’awarsu ta zama shugabannin majalisun dokokin ƙasar biyu.
Samun haɗin kan shugabancin majalisun biyu dai na da matuƙar tasiri wajen gudanar da ayyuka a ɓangaren shugaban ƙasa.
You must log in to post a comment.