Gidan Talabijin Na Liberty Ya Hau Tauraron DSTV

An zaɓi gidajen talabijin biyu daga yankin Arewacin Najeriya gidan talabijin na Liberty da Tozali matsayin wadanda za’a rinƙa ganin a tauraron dan Adam na DSTV da GOTV.

Wannan ya biyo bayan ganawar da gamayyar Kungiyoyin Arewa suka yi da shugabannin dake kula da Kamfanonin DSTV da GOTV a Tarayyar Najeriya a ranar Alhamis.

Tun farko da yake ƙarin haske akan ƙorafin da gamayyar kungiyoyin suka yi na cewar babu tashar talabijin ta ‘yan Arewa a jadawalin tashoshin DSTV da GOTV babban Darakta na Hukumar kula da kafafen yaɗa labarai na ƙasa NBC Ishaq Modibbo Kawu ya bayyana cewar tashar Liberty tuni tana kan GOTV.

Ganawar tasu wadda aka yi a dakin zartarwa na hukumar, ya samu halartar manya daga hukumar ta NBC da manyan wakilai daga gamayyar Arewa da wakilai daga kamfanin na DSTV.

Sakamakon taron ya amince da sanya tashoshi biyu daga yankin Arewa a jadawalin DSTV wadanda suka haɗa da Liberty TV da kuma Tozali TV wadanda suka cika ka’idojin da ake bukata, kuma kofa a buɗe take ga sauran tashoshin Arewa waɗanda suka cika ƙa’ida.

Matakin da kamfanin na DSTV ya ɗauka ya biyo bayan ƙorafin da gamayyar kungiyoyin Arewa suka yi ne na cewar Kamfanin ya yi watsi da tashoshin Arewa a jadawalin tashoshin dake kan tauraron dan adam duk da muhimmanci da suke dashi.

Gamayyar kungiyoyin sun koka dangane da hakan inda suka bayyana cewa rashin sanya tashoshin da ke magana da harsunan da Jama’ar Arewa ke amfani da shi ya taimaka wajen kara haifar da matsalar tsaro a yankin.

Labarai Makamanta