Gidajen Yada Labarai Na Arewa Sun Yi Kiran A Kauracewa Taron PDP

Kungiyar masu kafafen watsa labarai shiyyar Arewacin Najeriya NBMOA, sun yi kira ga ‘ya’yan Ƙungiyar da sauran kafafen yada labarai dake yankin da su kauracewa ɗaukar wani rahoto na taron PDP wanda aka shirya gabatarwa a ranar 31 ga wannan wata da muke ciki.

Daukar wannan mataki ya biyo bayan wani shiri ne da jam’iyyar PDP ta kuduri niyya na tsame Gidajen yada labarai na shiyyar arewa daga daukar labaran abubuwan da za su gudana a wajen taron.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa da kungiyar ta fitar wadda ta samu sanya hannun Shugaban riko na kungiyar Alhaji Abdullahi Yelwa Ajiyan Yawuri, kuma aka rarraba ta ga manema labarai a Abuja.

Sanarwar ta kara da cewar dukkanin wani kokari da kungiyar ta yi na tattaunawa da mashirya taron na PDP akan matsalar abin ya gagara. Bisa ga haka ƙungiyar ta dauki wannan mataki na kauracewa ɗaukar wani rahoto a wajen taron.

“Bisa ga haka muna sanar da dukkanin ‘ya’yan Ƙungiyar dake fadin yankin Arewa da su kauracewa ɗaukar rahoton taron na PDP”.

Mun fahimci wannan mataki da PDP ta dauka na ware gidajen yaɗa labarai na Arewa a taron ta, a matsayin alama ce babba dake nuna jam’iyyar zata nuna wata wariya ga yankin Arewa, a kokarinta na ganin ta dare karagar mulki a 2023.

Labarai Makamanta