Gayyatar Yariman Saudiyya Jana’izar Sarauniya Ya Haifar Da Surutai

Gayyatar da Birtaniya ta yi wa Yariman Saudiyya Mohammed Bin Salman zuwa jana’izar Sarauniya ya janyo zanga-zanga daga masu rajin kare hakkin bil-adama.

Wani rahoto da hukumar leken asirin Amurka CIA ta fitar ya nuna cewa Yariman na Saudiyya na da hannu wajen kisa tare da daddatsa gawar dan jaridar nan na Saudiyya Jamal Khashoggi a cikin karamin ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Santambul na kasar Turkiyya.

Sai dai a lokuta da dama Yariman na Saudiyya Muhammad Bin Salman ya musanta wannan zargi da ake yi masa tare da nesanta kanshi daga waɗanda ake zargi da aikata laifin.

Labarai Makamanta