Gaskiyar Magana Kan Mutuwar Auren Ado Gwanja

Majiyar mu ta Idon Mikiya da Shafin Labarai na Hausa tace wani labari da muke samu marar daɗin ji, akwai ƙishin-ƙishin ɗin cewa mawaƙi Ado Gwanja ya saki matar sa Maimuna, inda a wani bincike da Tashar YouTube ta Tsakar Gida ta gudanar ta gano cewa mawaƙin ya sauwakewa matar tashi, kuma sakin ba daya ba har saki uku.

Tashar Tsakar Gida sun tambayi dalilin saɓanin da ya haddasa sakin da tsawon lokacin da aka yi da yin sakin ba su samu wani gamsashshen bayani ba, amma dai sun tabbatar da rabuwar auren masoyan, wanda zai bakanta ran dubunnan masoyan su.

Maimuna Ta Cire Abubuwan Da Suka Shafi Ado Gwanja a Shafinta

Haka kuma a wani bincike da Tashar Tsakar Gida ta sake gudanarwa a shafin Maimuna, sun gano cewa ta cire duk wani abu da ya shafi Ado Gwanja a shafinta, hatta sunan Ms Ado Gwanja da ta sa ta cire ta sa sunan “Fashion Beauty”, haka shafin da take kasuwancin ta mai suna “Munat Gwanja Collection” shi ma ta canja shi zuwa “Munat Dan’auta Collection”.

Baya ga wannan, sanin kowa ne jarumin kan shirya kasaitaccen bikin “Birthday” ga matar tashi da ƴar sa duk shekara, amma wannan shekarar Maimuna ita kaɗai tayi ƴan hotunanta ta wallafa a shafin ta, kuma Ado Gwanja bai taya ta murna a shafin shi ko sashen tsokacin ta ba.

Bugu da ƙari a watan da ya gabata, mahaifiyar Maimuna ta rasu shi ma ta wallafa a shafin ta jaruman Kannywood na ta yi mata ta’aziyya, amma Ado Gwanja bai ce komai ba, haka kuma bai wallafa a shafinsa ba.

Haka kuma kowa dai yasan irin soyayyar da shakuwar da masoyan ke bayyanawa juna a shafukan sada zumunta, domin har hira BBC Hausa ta yi da Ado Gwanja, inda ya tabbatar da cewa ba zai yiwa matar sa kishiya ba.

Baya ga haka, kowa ya san yadda jarumin yake yawan wallafa hotunan matarsa tare da rubuta kalamai na soyayya da yake mata.

Haka ita ma an gano hotunan ta da bidiyo a wuraren shakatawa ba tare da siffa ta matar aure ba.

Labarai Makamanta