Gaskiyar Magana Akan Labarin Mutuwata -Ummi Zee-Zee

Tsohuwar jarumar masana’antar Kannywood, Ummi Zee-zee ta leko Instagram biyo bayan jita-jitar labarin mutuwar ta da ya cika gari, inda ta ce tana raye daram ba ta mutu ba.

A makon da ya gabata ne aka shiga rudu da mamaki biyo bayan samun labarin da ya fito daga shafinta na Instagram cewa ta rasu.

Sai dai tsohuwar jarumar ta ce ta shiga doguwar suma ne ba mutuwa ba, wanda hakan ya sa kawarta wadda a lokacin tana gidanta ne ta yi tsammanin ta rasu ne bayan ta yi ta zuba mata ruwa amma ba ta farfado ba.

A cewarta, “Ina mai ba ku hakuri dangane da labarin da kuka ji cewa na mutu. To da raina ban mutu ba. “Kawai dai na yanke jiki na fadi ne a gidan wata kawata a Kaduna, to sai ta yi zaton na mutu ne saboda ta yi ta zuba min ruwa ban farfado ba. “Shi ya sa ta bayyana wa duniya cewa na mutu sai da mijinta ya kaini asibiti ne aka duba, aka ce ban mutu ba.

“Saboda haka duk wanda ya nuna damuwarsa na jin labarin, ina godiya da kaunarsa. Sai dai ina fama da rashin lafiya matuka domin ina fama da ciwon matsananciyar damuwa.

Don haka ina bukatar addu’ar masoya,” inji Zee-Zee.

A kasan rubutun nata a Instagram, jama’a da dama sun tofa albarkacin bakinsu, wasu daga ciki har da jaruman fim na Kannywood.

Wani darakta a masana’antar Kanyywood Aminu S. Bono cewa ya yi, “Zango na uku ke nan, saura zango na hudu.” Shi kuma Darakta Sheikh Isa Alolo cewa ya yi “Abin mamaki shi ne ita da take rude amma ba ta manta lambobin sirrin wayarki ba, shi ne ta bude wayarki ta shiga Instagram dinki ta yi rubutun, maimakon ta yi a nata shafin.

“Ko da yake ba abin mamaki ba ne ko ita ba ta da shafin Instagram. Allah Ya kare mu, Ya kare mana imaninmu,” inji shi.

Labarai Makamanta