Gaskiyar Abin Da Ya Faru Bayan Sace Mu Da Aka Yi – Ɗaliban Ƙanƙara

Ɗaliban Makarantar Kimiyya ta Kankara, da ke jihar Katsina, su dari ukku da arba’in da hudu, da ‘yan bindigar suka sace a ranar juma’a da ta gabata, sun bayyana halin yadda sukai rayuwa a cikin daji tare da ‘yan bindigar da kuma yadda aka kawo harin tiryan-tiryan.

Wasu daga cikin daliban da aka tattauna da su a gidan gwamnati jihar Katsina, lokacin da jami’an tsaro na sojoji da yan sanda, suka hannanta su hannun Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, karkashin Shugaban Birget W D Idris da safiyar yau.

Daya daga cikin daliban wanda ya bayyanawa mana yadda aka sace su, Usman Galadima daga karamar hukumar Tsanyawa ta jihar Kano, ya fara da cewa “a daren mun kammala karatu daren, mun dawo dakin kwanan mu, kowa ya ci abinci,goma da rabi, sai muka fara jin harbe-harben karar bindiga, daga bakin kofar shigowa makarantar, ni har na haye bangon makarantar domin gudun tsira, sai aka ce mu dawo rabon tsautsayi. Sai suka hada mu wuri guda, suka kora mu daji, tafiyar har asuba muna tafiya, sai suka tsayar da mu, muka yi barci na awa guda. Haka muka isa dajin ga yunwa ga kishirwa, amma fa bugu, sai dai wanda ya nuna rashin ji. Suna ba mu Kuli-kuli kwara biyu duk rana, wani lokacin kuma dankali dan kadan. Gaskiya yau na ji dadi kwarai.

Shima wani dalibin ya bayyana wa wakilinmu cewa mun yi tafiya a kafa, mun kwana muna tafiya, suna ba mu wake da bai ida dafuwa ba, ko Kuli-kuli ko kuma dankali danye, Idan sun ji jirgi ya taho sai su ce mu kwan kwanta, muna gani wulgin jiragen da dare. Kuma muna shan ruwa da suke wanka. Mu dukkan mu dari ukku da arba’in, lokacin da za su sake mu sun dauko mu daga daji, ba su fito da mu cikin gari ba, kusa dai da garin ne da mashina sama da dari ukku.

Rayyanu Ahmad, Ina aji biyu na babbar sakandire, dan asalin karamar hukumar Sabuwa, wadanda suka zo makarantar ba su wuce su goma ba, muna fita wajen makarantar, muka iske wasu sun fi su dari biyu da mashina, suka dau yara kankana bisa babura, mu kuma muka tafi a kafa.

Shi kuwa Auwal Dabai ya bayyanawa mana cewa gaskiya mun sha wuya sosai, tsawon wadannan kwanakin da muka yi a rana sau daya suke ba mu abinci, ko Kuli-kuli kwara biyu ko danyen dankali ko wake, ruwa kuma sai dai mu sha na rafi. Ga shi ba mu da takalma, muna tafiya muna jin rauni, suna mana barazana da harbin bindugu, a kasa muke kwanciya kuma ba bargo ga sanyi. Gaskiya da aka kubutar da mu mun ji Dadi sosai.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yabawa gwamna Aminu Bello Masari, yadda yadda jajirce ganin an sako yaran. Kuma ya ba su kwarin gwiwa da ka da su kasa a gwiwa ko kasala sakamakon wannan iftila’i da ya fada masu, su ci gaba da nema ilmin domin rayuwar su ta nan gaba, inda ya ce shima kan shi makarantar kwana ya yi anan cikin garin Katsina, daga nan ya tafi aikin soja, har ya yi Shugaban kasa, daga nan ya shiga siyasa har ya cimma burinsa.

Yanzu haka dai yara na sansanin Alhazai na jihar Katsina, inda ake bincikar lafiyarsu, kuma kowane lokaci zuwa yanzu za’a damka su ga iyayen su.

Labarai Makamanta

Leave a Reply