Gasar Sarauniyar Kyau: An Nemi Na Cire Hijabi – Shatu Garko

Matashiyar da ta lashe gasar Sarauniyar kyau a Najeriya, Shatu Garko, ta yi ƙarin haske kan gwagwarmayar da ta sha a farkon tafiyarta a matsayin ta na mai sanya hijabi.

Shatu Garko mai shekaru 18 a duniya, wacce ta lashe gasar ta 44, inda ta lallasa abokan takara 18 wajen zama sarauniyar kyau mai hijabi ta farko ta bayyana hakan ne a wata hira da jaridar The Punch.

Ta bayyana cewa da farko ta ji tsoro saboda hijabinta. A cewarta, kamfanoni da dama sun ki aiki da ita saboda sun bata shawarar da ta cire hijabin idan tana so ta yi nasara a harkar tallace-tallace amma ta ƙi amincewa.

“Na fara tallata kayan ado ne tsawon kasa da shekara daya. Bayan na kammala makaranta, ina zaune a gida saboda annobar korona. Na tsani zama haka babu aikin yi, sai na yanke shawarar gwada tallata kaya.

“Aikin farko da nayi ya kasance da tangarda. Da farko sun dauke ni amma sai daga baya suka ce ina bukatar jagoranci mai inganci sannan suka yi watsi da ni.

“Sai dai kuma, wannan bai karya mun gwiwa ba. Maimakon haka, ya karfafa mun gwiwar sake daura damara.

Labarai Makamanta