Gasar Nahiyar Afirka: Najeriya Ta Lallasa Masar Da Ci Daya Mai Ban Haushi

Najeriya ta doke Masar da ci 1-0 a rukunin D na gasar cin kofin Nahiyar Afirka ta 2021.

Dan wasan Najeriya wanda ke buga wasa a Leicester City Kelechi Iheanacho ne ya zura kwallon a minti 30 da soma wasa.

Wasan shi ne mafi zafi kawo yanzu saboda girman ƙasashen a tarihin gasar cin kofin Afirka

An yi fafatawar ne a birnin Garoua na Kamaru da misalin ƙarfe huɗu na yamma agogon Najeriya da Kamaru.

Labarai Makamanta