Ganin Likita A Landan Al’adar Buhari Ce Tun Kafin Zama Shugaban Kasa – Shehu

“Babban abin da ya kamata jama’a su sani shine Buhari ya kasance yana zuwa duba lafiyar shi a birnin Landan tun kafin ya zama shugaban ƙasa a shekarar 2015, bisa ga haka babu dalilin surutan da jama’a ke yi akan fitar shugaban”.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana hakan lokacin da yake ƙarin haske akan fitar da Shugaban ƙasa Buhari ya yi zuwa birnin Landan domin ganin Likita.

Shehu ya bayyana hakan ranar Talata yayinda yake hira da manema labarai lokacin da jirgin Buhari ya tashi daga tashar jirgin Nnamdi Azikwe dake Abuja zuwa birnin Landan.

Ya kara da cewar “Shugaban kasa yana kokarin amfani da hutun bikin Easter ne. Lokacin da kowa ke hutu ne… Saboda haka zai yi amfani da lokacin wajen duba lafiyarsa.” “Wannan abu ne wanda ya dade yana yi shekara da shekaru tun kafin ya hau mulki, duk shekara yana ganawa da Likitocinsa.”

An ruwaito cewa shugaba Muhammadu Buhari ya tashi daga tashar jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe dake Abuja domin zuwa kasar Birtaniya.

Hadimin Buhari kan gidajen talabijin da rediyo, Buhari Sallau, ya bayyana hakan da misalin karfe 3 na ranar jiya.

Labarai Makamanta