Ganduje Ya Sulhunta Ɗangote Da BUA

Tun a farkon makon da ya gabata ne aka samu rashin fahimtar juna a tsakanin jigajigan attajiran ‘yan kasuwan Najeriya Aliko Dangote da Isiyaka Rabi’u mai kanfanin Bua Wanda dukansu ‘yan asalin jihar kano ne.

An samu nasarar sulhunta attajiran biyu ne Bayan wanu zaman fahimtar juna da Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR, yayi tsakanin shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote da shugaban kamfanin BUA, Alhaji Abdussamad Isyaka Rabi’u bisa kuskuren fahimta da suka samu akan harkokin kasuwancin su.

Bayanin haka na kunshe cikin wata sanarwa da mai taimakawa gwamnan kan harkokin yada labarai Abba Anwar ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

Ya ce: “Hakan ce tasa Gwamnan ya gayyaci yan kasuwar biyu kasancewar su yan asalin jihar Kano da kuma irin gudunmawar da suke baiwa jihar Kano da kasa baki daya.”

A cewarsa, manyan attajiran biyu sun karyata rahoton cewa Dangote ya bukaci Isyaka Rabiu su tada farashin sukari.

Wadanda suka hallarci zaman sun hada da Hamshakin Dan kasuwa Alhaji Aminu Alhassan Dantata, ministan ciniki da masana’antu Hon. Niyi Adebayo, wakilin Kano, Sarkin Dawaki Babba Alhaji Aminu Babba Dan Agundi, shugaban hukumar NEPZA Hon. Adamu Fanda da shugaban majalisar limaman Juma’a Sheikh Nasiru Adam limamin masallacin Ahmadu Tijjani dake kofar Mata.

Labarai Makamanta