Ganduje Ya Biya Wa Daliban Da Ke Karatu Waje Sama Da Naira Biliyan Biyu

Gwamnatin Jihar Kano, karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ta biya wa daliban da ke karatu Kasar Sudan bashin sama da Naira Bilyan biyu. Gwamnatin ta Ganduje ta gaji tulin wannan bashi ne daga tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Gwamnan Jihar Kanon ne ya bayyana haka a lokacin da kwamatin amintattu na Jami’ar Farfesa Ibrahim Ghandour su ka ziyarce shi a ranar Talatar da ta gabata.

Ganduje ya kara da cewa, “mun gaji basukan wadannan dalibai daga Gwamnatin da ta gabata, inda ta bar wa wannan Gwamnati tulin basussukan da ba ta biya ba, amma sakamkon kyakkyawar fahimta tsakanin Hukumar Jami’ar da Gwamnatin Jihar Kano, yasa muka samu damar biyan wadannan basuka wanda hakan ya baiwa Dalibanmu damar kammala karatunsu.”

Gwamnan, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Dakta Nasiru Yusif Gawuna, ya cigaba da cewa, wannan gwamnati ta biya kusan kaso 80% na daliban da ke karatu a kasashen Indiya da Cyprus, wanda su ka gada daga Gwamnatin da ta gabata ta Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso.

Haka zalika, “kwana-kwanan nan wannan Gwamnati ta sake biyan sama da Naira Milyan 300, ga Daliban da ke karatu a Jami’ar Cyprus, domin bai wa Daliban damar kammala karatunsu”.

Daga nan ne kuma, sai ya kalubalanci duk wani wanda ke siyasantar da harkokin ilmin Jihar Kano da cewa, wannan dabi’ar ba za ta amfanar da Jihar da ma kasa baki daya ba.

“Ba wai siyasantar da harkokin ilmi ne abin da ya kamata a yi ba, duk wanda ke kokarin kalubalantar wani abu na Gwamnati, kamata ya yi dole ya aminta tare da gabatar da kalubale mai dalili, domin ba mu ce komai namu 100 bisa 100 yake ba, amma dai yanzu mun yi hakuri tare da kokari kwarai da gaske wajen biyan wadannan basussuka”, a cewarsa.

Da ya ke bayyana gamsuwarsa da kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin Kasar ta Sudan da Nijeriya, Gwamna Ganduje ya tabbatar wa da Hukumar Jami’ar ta El-Razi cewa, Daliban Jihar Kano za su ci gaba da nuna kyakkyawar dabi’a a lokacin zamansu a Makarantar. Da yake tsokaci a kan Digirin girmamawa da Jami’ar ta ba shi, Gwamnan ya bayyana lambar girmamawar a matsayin ta al’ummar Kano ce bakidaya.

Haka nan, shi ma anasa jawabin Ghandour cewa ya yi, suna jadadda farin cikinsu bisa kyakkyawar dangantakar da ke gudana tsakanin kasashen biyu musamman cikin shekaru masu yawan gaske. “Mun zo Jihar Kano ne domin wakiltar wannan Jami’a da kuma neman amincewar Gwamna Ganduje, domin karrama shi da Digirin girmamawa.

“Jami’ar El-Razi yanzu ta cika shekara 23 ta na yaye Dalibai a fannin hada maganunuwa, sannan Jami’ar kan karrama wasu fitattun mutane a duniya baki daya. Ya ce za a gudanar da wannan bikin girmamawa a ranar 26 ga watan Agustan shekarar 2019 mai zuwa.”

Related posts