Ganduje Na Neman Rayuwata – Jaafar Jaafar


Ɗan jaridan da ya fitar da jerin bidiyon da ke zargin Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da karɓar cin hanci ya ce ya bar Nijeriya ne saboda ba shi da ƙwarin gwiwar hukumomi za su kare rayuwarsa.

Cikin hirarasa da BBC Hausa daga Ingila, Ja’afar Ja’afar ya ce zai ci gaba da neman mafaka a Birtaniya tare da iyalinsa har sai ya samu tabbacin za a kare rauywarsa idan ya koma Najeriya.

Kazalika, ya yi zargin cewa cin hanci da rashawa a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari sun ƙara ta’azzara, inda ake yaƙar masu fallasa badaƙalar maimakon ainihin masu aikata cin hancin.

A shekrar 2018 ne mawallafin jaridar Daily Nigerian ɗin ya saki wasu bidiyo da ke zargin cewa Gwamna Ganduje ne yake karɓar damman daloli daga hannun wani ɗan kwangila a matsayin cin hanci.

Sai dai gwamnan ya sha musanta zargin yana mai cewa ƙirƙirar bidiyon aka yi.

Labarai Makamanta