Gamayyar Kungiyoyin Arewa Sun Yi Kiran Kauracewa Kallon DSTV

Gamayyar kungiyoyin cigaban Arewa sun yi kira da babbar murya ga jama’ar Arewa da su kauracewa kallon tashoshin tauraron dan Adam na DSTV sakamakon yadda kamfanin ke nuna kyama da wariya ga jama’ar yankin na Arewa.

Kungiyoyin sun yi wannan kiran ne a cikin wata takardar sanarwa da suka fitar wacce ta samu sanya hannun Sakataren gamayyar kungiyoyin Balarabe Rufa’i kuma aka rarraba ta ga manema a Kaduna.

Kungiyoyin sun ƙara da cewar a tsawon lokacin da Kamfanin na DSTV ya ɗauka yana gudanar da harkokin shi a Najeriya tare da samun riba ta Miliyoyin kuɗi a hannun ‘yan Najeriya musamman ‘yan Arewa, amma abin takaici kamfanin ya mayar da hankali wajen sanya tashoshin talabijin na Kudancin Najeriya, wanda lallai akwai buƙatar a surka ta hanyar sanya gidajen talabijin da rediyo mallakin ‘yan Arewa a ciki.

Gamayyar kungiyoyin sun ce tuni suka aike da takardar korafi ga shugaban hukumar kula da kafafen yaɗa labarai na ƙasa, da shugaban kwamitin majalisar dattawa akan harkar yaɗa labarai da sauran hukumomin dake da ruwa da tsaki akan harkar yaɗa labarai a nahiyar Afirka.

Kungiyoyin sun bayyana cewar Kamfanin DSTV na sanya shirye shirye da labaran duniya da wasanni a tashoshin talabijin kimanin 135, amma a ciki babu gidan talabijin guda mallakar ɗan Arewa.

“Da gangan DSTV ta yi watsi da tashoshin talabijin mallakar ‘yan Arewa waɗanda suke gudanar da harkokin su cikin harshen Hausa da turanci wanda Miliyoyin jama’a a sassa daban daban na ƙasar har da makwabta ke amfana dasu”.

Labarai Makamanta