Gamayyar Kungiyoyin Arewa Sun Yi Karar A Raba Najeriya

Rahoton dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Wata tawagar Ƙungiya Arewacin Najeriya ta nemi babban kotun tarayya reshen Abuja da a roki ‘yan majalisu a Najeriya su cire yankin kudu maso gabas daga Najeriya kafin aiwatar da gyare-gyaren kundin tsarin mulkin Najeriya.

Nastura Ashir Shariff, Balarabe Rufa’I, Abdul-Aziz Sulaiman da Aminu Adam sun shigar da batun kotu tare da bayyana cewa, hakan zai taimaka wajen rage faruwar rikice-rikice da zubar da jinane daga ‘yan awaren yankin.

Sun yi ikirarin cewa ba sa son a maimaita yakin basasar da aka yi a Najeriya tsakanin 1967 zuwa 1970 wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyin al’ummar kasar da yawansu ya kai biliyoyin Naira.

Wadanda ake magana akansu a cikin karar sun hada da Babban Lauyan Tarayya (AGF), Shugaban Majalisar Dattawa, Kakakin Majalisar Wakilai da Majalisar Dokoki ta Kasa.

Sai dai a wani martani na gaggawa, lauyoyin yankin kudu maso gabas masu magana da harshen Igbo a Najeriya sun nemi kotu ta hada su a jerin wadanda ake magana a kansu.

Lauyoyin da ke karkashin wani Babban Lauyan Najeriya, Cif Chuks Muoma, Ukpai Ukairo, Ebere Uzoatu da Hon Obi Emuka suna neman kotu ta ba su izinin shiga karar a matsayin wakilan al’ummar yankin Kudu maso Gabas.

Sun shigar da wannan batu a ranar Litinin ta hannun Victor Onweremadu ya shigar, inda suka bayyana cewa, bukatar kungiyoyin Arewan ya dace da bukatarsu, wadda suka dade suna nema.

Dangane da wannan bukata, kotu a karkashin mai shari’a Inyang Eden Ekwo ta sanya ranar 1 ga watan Nuwamba domin saurarar korafe korafen.

Labarai Makamanta