Fursunoni Sun Fi ‘Yan Yi Wa Kasa Hidima Gata A Najeriya – NYSC

Hukumar kula da masu yi wa kasa hidima NYSC ta koka kan yadda fursunonin da ke karkashin kulawar ma’aikatun hukumar gyaran hali ta Najeriya ke samun na abinci fiye da na ‘yan yi wa ƙasa hidima NYSC.

Babban Darakta Janar na NYSC, Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim, wanda ya bayyana haka a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisa don kare kasafin kudi a ranar Larabar da ta gabata, ya ce ana ba ‘yan NYSC abincin da ya kai na N217.

Don haka, ya bukaci Majalisar Wakilai da ta samar da kari a kason abinci a kasafin kudin shirin na 2022.

A ranar 27 ga Oktoba, 2021 ne kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin cikin gida ya kara yawan kudin ciyar da fursunoni daga naira 450 da take ba kowane mutum a yanzu zuwa mafi karancin naira 1,000 a kowace rana.

Jami’an NCS sun kasance a majalisar dattawa domin kare kasafin kudin hukumar na 2022, inda suka bada shawarar a kara kudaden ciyarwar a rana zuwa N750. Kwamitin, ya bayyana adadin a matsayin wanda bai isa ba kuma ya kara yawansa daidai da yanayin tattalin arzikin da ake ciki a yanzu, inda ya yi alkawarin yin nazari a kan kudin ciyar da fursunoni daga N450 zuwa N1000 a kowace rana.

A nasa jawabin, Ibrahim, wanda ya bayyana cewa al’ada ce ta farko da ya gabatar da kasafin ga kwamitin, ya ce kasafin kudin NYSC ya ci gaba da kasancewa a yadda yake a shekarun da suka gabata.

“Kalubalenmu shi ne a fannin ciyar da abinci. Amincewa da kasafin kudin ciyar da kowane dan bautar kasa shine N650, wanda bai wadatar ba. A lokacin da za ka raba shi zuwa abinci uku (a rana), wato Naira 216 a kowane kari.

Don haka muna kira ga wannan kwamiti da ta taimaka mana. “Ko a kwanan baya ma a ma’aikatar harkokin cikin gida an kara ciyarwar fursunoni zuwa Naira 1,000. Don haka, idan har za mu iya ciyar da masu laifi da N1,000, wadanda suka kammala karatunmu suna sadaukar da rayuwarsu wajen yi wa kasarmu hidima… Ina rokon wannan kwamiti ya yi wani abu a kai.”

Labarai Makamanta