Fulani Suka Yi Yunkurin Hallaka Ni – Ortom

Mai girma Gwamnan jihar Binuwai Mista Samuel Ortom, ya fito fili ya zargi ‘Yan Bindigar Fulani da yunƙurin hallaka shi a wani mummunan hari da suka kai wa ayarin motocin shi da safiyar wannan rana ta Asabar.

Ortom ya kara da cewa kimanin mutum 15 wadanda suka kai masa harin ɗauke da muggan makamai sun bibiyeshi tare da auna motar da yake ciki da manyan Bindigogi da niyyar gamawa da shi.

Tun farko an bayyana harin da wasu ‘yan bindiga da ake zargin Fulani ne suka kai lokacin da suka bude wuta kan ayarin motocin gwamnan jihar Binuwai Samuel Ortom.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa an bude wa ayarin gwamnan wuta ne a ranar Asabar, 20 ga Maris, lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Makurdi babban birnin Jihar.

An tattaro cewa Ortom na a hanyar dawowa daga Gboko lokacin da lamarin ya faru.

Samuel Ortom dai ya dade yana zargin Fulani da aikata ayyukan ta’addanci a faɗin Jihar ta Binuwai, inda a kwanakin baya aka samu takaddama da takwaranshi Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad akan matsayin ɗaukar muggan makamai da Fulani makiyaya ke yi.

Labarai Makamanta