Fitina Wadda Ta Zarce Matsalar Tsaro Na Fuskantar Najeriya – Ministan Tsaro

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan tsaro, Bashir Magashi, ya bayyana cewa ƙaruwar matsalar tsaro a Najeriya yana haifar da ƙarancin abinci, kuma hakan sabuwar barazana ce dake tunkarar kasar.

Ministan ya faɗi haka ne ranar Litinin a wurin bude wani taro da hukumar tsaro ta fasaha (DIA) ta shirya a Abuja. Ministan yace hare-haren ƙungiyar Boko Haram da ISWAP, da kuma ƙalubalen yan bindiga a Arewa ya zama wata babbar barazana ga tsaron Najeriya.

Hakanan Magashi yace satar ɗanyen mai a kudu maso kudu da kuma masu fafutukar ɓallewa a kudu maso gabas, da fitinar ‘yan awaren Yarbawa masu hankoron kafa yankin Oduduwa suma wata barazana ce ga Najeriya.

“Abin takaicin shine wannan barazana da ake fama da ita na cigaba da zama ƙalubale ba wai ga tsaron ƙasa da tattalin arziki ba kaɗai, sabuwar barzanar ƙarancin abinci ce” “Matsalar abinci shine ya jawo tashin gwauron zabi na farashin kayan abinci a faɗin kasa wanda hakan ya zama wata sabuwar barazana.” “Wannan yasa ya zama wajibi hukumomin tsaro su haɗa kai wajen dakile matsalolin kuma su nemo sabbin hanyoyin gane wasu kalubale da ka iya tasowa a gaba.”

Magashi ya ƙara da cewa nasarorin da jami’an tsaro suka samu kwanan nan yasa yan tada ƙayar baya sama da 14,000 ne suka miƙa wuya tare da aje makamansu.

Labarai Makamanta