Filato: ‘Yan Bindiga Sun Yi Gaba Da Babban Basarake

Labarin dake shigo mana daga jihar Filato na cewa wasu gungun ‘yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun sace babban basaraken kauyen Tal da ke karamar hukumar Pankshin.

An rawaito cewa basaraken da aka sace shi ne Ngolong Tal, Alhaji Dabo Gutus. Lamarin ya faru ne misalin karfe daya na dare a ranar Litinin.

Wani mazaunin kauyen ya ce mutane na ta kokarin kiran ‘yan bindigar don sanin halin da basaraken yake ciki.

Prince Dakup Ezra, wanda yake wakiltar kauyen Panshin a majalisar dokoki, ya yi kira a kwantar da hankali, yana mai cewa babban burinsu shi ne a kubutar da basaraken.

Labarai Makamanta