Filato: Shugabannin APC Sun Jaddada Goyon Bayan Lalong Kan Takarar Shugabancin Kasa

Shugabannin jam’iyyar APC na jihar Filato sun kare kudirinsu na mara wa gwamnan Jihar Samuel Lalong baya ya nemi kujerar Shugabancin Najeriya a zaɓen 2023 dake tafe.

Yayin ganawarsu a Jos babban birnin Jihar ranar Lahadi domin tattauna kudirin mara wa Lalonga baya, Shugabannin sun kuma tattauna kan rikicin dake wakana a majalisar dokokin jihar.

A taron nasu, shugabannin sun bayyana cewa Lalong yasan hanyoyin shawo kan matsalolin siyasa, hakan yasa rikicin majilisar bai yi muni ba.

Da yake zantawa da manema labarai a madadin shugabannin jim kaɗan bayan taronsu, Saleh Mandung Zazzaga, yace gwamna Lalong zai ɗaga martabar ƙasar nan zuwa inda mutane basa tsammani shi yasa suke rokonshi ya amince ya fito takarar.

A cewarsa sun yi wannan hasashen ne duba da nasarorin da ya samu na rikice-rikice da kuma yadda ya saita sabanin da ake samu na banbancin ƙabila ko addini a jihar Fitalo.

Ya ƙara da cewa duk da rikicin da ake samu nan da can, gwamnan bai yi ƙasa a guiwa ba wajen jawo kowane bangare a cikin gwamnatinsa. Yace: “Lalong ne yake jagorantar ƙungiyar gwamnonin Arewa, kuma mafi yawan mutanen wannan yanki da ma na waje na yaba wa da tsarin mulkinsa.”

Lalong yana da kwarewar da Najeriya ke bukata Zazzaga ya kara da cewa gwamna Lalong yana da duk wata kwarewar siyasa wajen ɗaukaka Najeriya zuwa babban matsayi da kuma ƙara dankon haɗin kai.

Labarai Makamanta