Filato: Lalong Ya Ware Milyan 60 Domin Sayen Ragunan Layya

Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya ware zunzurutun kudi Naira Miliyan 60 domin sayen ragunan layya da shinkafa da za a raba wa al’ummar Musulmin jihar, albarkacin hidimar Babbar Sallah da za a gudanar.

Gwamnan ya mika alhakin tabbatar da rabon wadannan ragunan layya ne ga Farfesa Garba Sharubutu, inda ya ba da umarnin a tabbatar da an raba wa Musulmi da ke dukkan fadin jihar.

Kawo lokacin hada wannan rahoto dai an kafa kwamitoci da za su kula da yadda rabon zai kasance a matakin shiyya shiyya da kananan hukumomi.

Wani mamba da ke cikin wannan kwamiti wanda ya nemi a sakaya sunansa, saboda ba shi ne ke da alhakin magana da ‘yan jaridu ba, ya tsegunta cewa, daga cikin tsarin da aka yi don ganin sakon ya isa ga dukkan bangarorin Musulmin jihar, shi ne ta hannun mikawa ga kungiyoyin Musulmi, wadanda su ne suka san mabiyansu da yadda sakon gwamnan zai isa gare su.

Fatan da Musulmi a Jos babban birnin jihar ke yi shi ne, Allah ya sa sakon ya isa ga talakawan da ake nufin taimakawa ba jami’an gwamnati ko wadanda ba Musulmi ba, kamar yadda yake kasancewa a mafi yawan lokuta irin wannan.

Malam Buhari Bukar Bello shugaban kungiyar Musulmi ‘yan jarida ta MMPN a Jihar Filato ya bayyana takaicinsa na yadda duk da kokarin da gwamnati take yi na sauke nauyin al’umma da ke kanta, amma wasu tsirarun mutane suna rub da ciki a kai, ta yadda sai dai ka ji labarin an yi rabo amma ka rasa wadanda abin ya isa gare su, sai ‘yan kalilan.

Wata jigo a kungiyar mata Musulmi ta FOMWAN Hajiya Fatima Suleiman ta ce, duk da yake ba kowa ne zai samu ragon layya ko buhun shinkafa ba, amma ta yi kira ga wadanda aka dorawa alhakin wannan rabo su ji tsoron Allah, su yi rabon da jama’a masu karamin karfi za su san lallai an yi gaskiya.

Gwamnatin Jihar Filato ta kasance tana yin wannan tallafi duk shekara ga al’ummar Musulmi, don a samu damar yin bukin sallah cikin walwala.

Related posts