Shugabannin Gidajen Talabijin da Rediyo Shiyyar Arewa sun koka dangane da wariyar da jam’iyya mai mulki ta APC da Kwamitin yakin neman zaben shugaban ƙasa na jam’iyyar ke nuna musu, inda suke fifita gidajen Talabijin da Rediyo na Kudancin Najeriya ta hanyar ba su tallace tallace, amma na yankin Arewa ko oho.
“Mun gano cewar Gidajen Talabijin da Rediyo na kudancin Najeriya musamman yankin Kudu maso yamma, su ake fifitawa ta hanyar ba su tallace tallace na jam’iyyar APC da kuma yaƙin neman zaben shugabancin ƙasa na Tìnubu, su kuma ‘Yan Arewa an yi watsi dasu”.
Sun kara da cewar a fili yake jam’iyya mai mulki ta APC da Gidajen Yaɗa Labarai na kudancin kawai suke aiki, yayin da suka yi watsi da na yankin arewa gaba daya.
Shugabannin Gidajen yada labaran na Arewa sun bayyana cewar tuni suka aike da takardar korafi zuwa ga shugaban jam’iyyar APC na kasa Sanata Abdullahi Adamu da kuma kwamitin yakin neman zaben takarar Tinubu kan halin da ake ciki, da kuma kira a gare su da suyi gaggawar daukar mataki ba tare da bata wani lokaci ba.
Shugabannin Gidajen yada labaran na Arewa sun bayyana wannan mataki da aka ɗauka na yin watsi da gidajen Talabijin da Rediyo na Arewa a harkokin jam’iyyar APC a matsayin wata manufa ta keta mutuncin jama’ar arewa idan su ka yi kiran a gaggauta ɗaukar matakan shawo kan matsalar ko kuma kafatanin Gidajen Talabijin da Rediyo na Arewa su kauracewa dukkanin tarukan jam’iyyar musanman yaƙin neman zaben shugaban ƙasa na APC gaba ɗaya.
Shugabannin Gidajen yada labaran na Arewa sun sanar da hakan ne a takardar sanarwar da suka fitar wadda aka rarrabata ga manema labarai a birnin tarayya Abuja.
You must log in to post a comment.