Farin Jinin APC Gaba Yake Yi A Kullum – APC

Jami’iyyar APC mai mulki a Nijeriya ta bayyana cewa zuwa yanzu tana da Membobin da suka yi rijista sama da miliyan arba’in wanda a baya miliyan sha biyu ne.

Sakataren Kwamitin Rikon Kwaryar Jam’iyyar APC na kasa, Mista John James Akpan Udo-Edehe ya bayyanawa manema labarai haka, a lokacin da suka karbi bakuncin ambasadajin da Shugaban Kasa Muhammadu ya nada, yan siyasa a helkwatar jam’iyyar APC dake Abuja.

Sakataren jam’iyyar APC ya ce kafin mu fara yi wa sabbin membobin mu rijista da kuma sabunta ta, wanda mu ka kammala kwanan nan, muna da yawan membobi miliyan sha biyu kacal, wanda yanzu haka muna da Membobi miliyan arba’in, saboda irin jajircewar shugabanni rikon jam’iyyar APC na kasa karkashin gwamna Mai Mala Buni.

Labarai Makamanta