Farashin Mai: Sai Mun Kassara Najeriya Da Yajin Aiki – Ƙungiyar Ƙwadago

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kungiyar Kwadago NLC, ta dage cewa ma’aikata da talakawa ba za su sake amincewa da karin farashin man fetur da gwamnatin kasar ke shirin yi ba.

A sakonsa na barka da arziƙin shigowa sabuwar shekara, shugaban kungiyar ta NLC Ayuba Wabba ya ce har yanzu gwamnati ba ta ja da baya a kan aniyar ta ta ba.

‘’To, kungiyar kwadago ta bayyana matsayinta a kan wannan batu. Mun shaida wa gwamnati a fili cewa ƴan Najeriya sun sha wahala sosai kuma ba za su sake jure irin wannan ba’’ inji shi.

NLC dai ta ce a shirye take ta durƙusar da al’amura ciki a Najeriya matsawar gwamnati ta sake bijiro da wannan batu.

Labarai Makamanta