Faransa Ta Kai Zagaye Na Biyu A Gasar Cin Kofin Duniya

Tawagar ƙwallon ƙafa ta Faransa mai riƙe da Kofin Duniya ta zama ta farko da ta samu nasarar zuwa zagaye na gaba a gasar bayan ta lallasa Denmark 2-1.

Tun a ranar Juma’a Qatar mai masaukin baƙi ta zama ƙasa ta farko da aka yi waje da ita daga gasar.

Kylian Mbappe ne ya ci wa Faransa ƙwallayen, inda mai tsaron bayan Denmark Andreas Christensen ya ci wa ƙasarsa ɗaya.

Kazalika, a ɗazu an yi gumurzu tsakanin Saudiyya da Poland inda Poland ɗin ta doke Saudiyya 2-0.

Haka kuma an fafata tsakanin Australiya da Tunisiya a wasan da Australiyar ta yi nasara da 1-0 .

A halin yanzu dai ana karawa ne tsakanin Argentina da Mexico a wasan Rukuni na C.

Labarai Makamanta