Fallasa Masu Daukar Nauyin Ta’addanci: Gwamnan APC Ya Yi Amai Ya Lashe

Rahoton dake shigo mana daga Jihar Imo na bayyana cewar Gwamnan jihar Hope Uzodinma, ya gaza bayyana sunayen masu ɗaukar nauyin ta’addanci kamar yadda ya yi alkawarin yi a ranar Talata 4 ga watan Janairu.

Jaridar Vangaurd ta bibiyi jawabin gwamnan a wurin taron masu ruwa da tsaki na jihar Imo, wanda ya gudana a gidan gwamnatin jiha. Amma Uzodinma ya yi kira ga sanata mai wakiltar jihar Imo ta yamma Rochas Okorocha, ya kyale shi haka nan ya jagoranci jihar Imo cikin kwanciyar hankali.

“Banbancin tsohon gwamna, Okorocha, da sauran waɗan da suka jagorancu jihar Imo shi ne, yana son ya cigaba da mulkin jihar nan bayan ya bar ofis.” “Okorocha ne kaɗai gwamnan dake son mallake wannan jihar shi kaɗai.

Ya kamata ya bar ni na mulki wannan jihar a matsayin gwamna.” “Ko babu komai na girme shi, akalla ya dace ya rinka girmama ni. Ba zai yuwu mu bar mutum ɗaya ya cigaba da tafiyar da harkokin jihar mu ba.”

Maimakon bayyana sunayen, gwamnan yace zai kyale hukumomin tsaro su kammala binciken su kan masu ɗaukar nauyin rashin tsaro a jihar. Sai dai ya baiwa mutanen jihar Imo hakuri, sannan yace: “Ya kamata mu bar hukumomin tsaro su yi aikin su, su kammala bincike kuma su bayyana sunayen masu ɗaukar nauyin rashin tsaro, kuma su kame su baki ɗaya.”

Labarai Makamanta