Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Tir Da Rikicin Filato

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kisan baya-bayan nan da aka yi a Jihar Filato inda ya ce bai kamata yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimmawa ba tsakanin Fulani da Irigwe ta shashance ba.

A wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan harkokin yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya fitar, Shugaba Buhari ya nuna rashin jin daɗinsa kan kashe-kashen da aka yi a Ƙaramar Hukumar Bassa ta Filato inda shugaban ya buƙaci al’ummomin yankin da kuma musamman majalisar da ke kula da harkokin addini ta jihar da ta yi duk mai yiwuwa domin ganin yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimmawa ba ta rushe ba.

“Duk al’ummar da ta ɗauki doka a hannunta sai ta ce wai tana ramuwa ne. A matsayin al’umma, irin wannan rikicin ba shi da muhalli. Ba za a yarda da wannan ba,” in ji Shugaban.

Ranar Talata da dare ne dai aka kai hari a ƙauyukan Ancha da Irigwe duk da ke Ƙaramar Hukumar Bassa inda aka kashe mutum 18.

Labarai Makamanta