Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da abin da ya kira ‘kisan rashin hankali” da wasu ‘yan sanda da ke bakin aiki suka yi wa wata lauya mai suna Omobolanle Raheem ranar Kirsimeti.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Malam Garba Shehu ya fitar, shugaba Buhari ya ce ya yi matuƙar kaɗuwa da jin labarin kashe lauyar,.
Sannan kuma shugaban ya umarci hukumomin ‘yan sanda da su ɗauki tsattsauran mataki kan waɗanda suka aikata wannan ta’asa.
A wata mai kama da wannan ita ma hukumar kula da aikin ‘yan sanda ta Najeriya ta yi Allah wadai da kisan lauyar.
A cikin wata sanarwa da ta fitar mai ɗauke sa hannun shugaban sashen hulɗa da jama’a na hukumar Ikechukwu Ani, hukumar ta ce tana buƙatar rahoto kan kisan daga hukumar ‘yan sandan, da kuma kiran bayar da horo ga ‘yan sanda kan yadda za a riƙe makamai.
Tuni dai shugaban rundunar ‘yan sanda ta ƙasa Usman Alƙali Baba ya bada umarnin kamowa gami da gurfanar da jami’in ɗan sandan da ake zargi da yin kisan domin fuskantar hukunci.
Marigayiyar ta rasa ranta ne a ranar Kirsimeti akan hanyar su ta dawowa daga Coci tare da mijinta lokacin da ɗan sandan ya yi harbin da ya kai ga rasa ranta.
You must log in to post a comment.