Fadar Shugaban Ƙasa Ta Musanta Labarin Rashin Lafiyar Osinbajo

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Fadar shugaban kasa tayi martani ga wani rahoto dake bayyana cewa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo bashi da lafiya kuma an gan shi a asibitin Reddington dake Legas a ranar Asabar, 22 ga watan Mayu.

Kamar yadda Sahara Reporters suka ruwaito, ganin Osinbajo a asibitin ya janyo tashin hankula da kuma tambayoyi daban-daban na dalilin zuwan mataimakin shugaban kasan asibitin.

A yayin karin bayani, Sahara Reporters tace “Abinda yasa ‘yan Najeriya suka damu da ganin mataimakin shugaban kasan a asibitin Reddington dake Legas shine ganin bai halarci jana’izar marigayi shugaban sojin kasa na Najeriya ba, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da sauran jami’ai 10 wadanda suka yi hatsarin jirgin sama a Kaduna.”

Amma kuma, Laolu Akande, babban mai bada shawara a fannin yada labarai ga mataimakin shugaban kasar ya musanta rahoton a wata wallafa da yayi a Twitter ranar Litinin 24 ga watan Mayu.

Akasin tunanin jama’a da yadda Sahara Reporters ta ruwaito, Akande yace mataimakin shugaban kasa yaje asibitin Legas ne domin duba ingancin lafiyarsa kamar yadda yake yi duk shekara. Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasan yace Osinbajo ya dawo Abuja da yammacin ranar Asabar, 22 ga watan Mayun 2021.

Labarai Makamanta