Fadar Sarkin Musulmi Ta Ayyana Yau Litinin Daya Ga Sha’aban

Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar koli kan Harkokin Addinin Musulunci (NSCIA), Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ayyana ranar yau Litinin 15 ga Maris, a matsayin ranar farko ta watan Sha’aban 1442AH.

Sarkin Musulmi Abubakar, ya bayyana hakan ne a cikin wata takardar sanarwa da Farfesa Sambo Junaidu, shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini, majalisar masarautar ta Sokoto ya fitar.

“Kwamitin Shawara na Majalisar Masarautar Musulunci kan harkokin Addini tare da hadin gwiwar kwamitin kula da wata na kasa ba su samu wani rahoto da ke tabbatar da ganin jinjirin watan ba.

“Wannan na sabon watan Sha’aban din 1442AH kenan, a ranar Asabar 13 ga Maris, wanda yayi daidai da ranar 29 ga Rajab 1442AH. “Saboda haka, Lahadi 14 ga Maris, ta zama 30 ga Rajab 1442AH yau Litinin kuma ɗaya ga watan sha’aban.

Sanarwar ta ce: “Sarkin Musulmi ya karbi rahoton, kuma bisa haka ya ayyana ranar Litinin 15 ga Maris, a matsayin ranar 1 ga watan Sha’aban 1442AH.”

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Sha’aban shi ne wata na takwas a kalandar Musulunci, wanda ke zuwa kafin fara azumin watan Ramadan. Sha’aban shine watan karshe kafin watan Ramadan da Musulmai suke amfani dashi don tantance ranar farko ta azumi.

Labarai Makamanta