EndSARS: Ba Za Mu Tursasa Wa Jami’anmu Komawa Aiki Dole Ba – Hukumar ‘Yan Sanda

Hukumar ‘yan sandan Najeriya ta bayyana cewa ba za ta tursasa ma kowane jami’in dan sanda komawa bakin aiki ba, bayan kammala ƙazamar Zanga-Zangar EndSARS da ta addabi Kudancin Najeriya.

Hukumar ‘yan sandan ta bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 1 ga watan Nuwamba, a cikin wata sanarwa daga Shugaban harkokin labaranta da hulda da jama’a, Ikechukwu Ani ya sanya wa hannu kuma aka rarraba ta ga manema labarai.

Jawabin martani ne ga wata jarida da ta wallafa cewa hukumar ta yi barazanar korar duk jami’an da suka ki dawowa bakin aiki.

Hukumar ta ce rahoton kanzon kurege ne, cewa zai zama rashin hankali tsantsa ga hukumar idan ta kori wani jami’in ta da ya ki komawa aiki.

A baya dai mun ji yadda zanga-zanga a sassa daban-daban na kasar ya koma rikici bayan sojoji sun harbi masu zanga-zangar lumana a Lekki toll gate da ke jihar Lagas.

Tuni dai ‘yan sanda da dama suka yi watsi da ayyukansu bayan barkewar rikicin.

A cikin jawabin Mista Ani, ya ce abunda kawai hukumar za ta iya yi shine ta roki jami’an yan sanda su koma bakin aiki duba ga yawan rayukan da yan sandan suka rasa a yayin zanga-zangar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply