El Rufa’i Ya Bada Laƙanin Daƙile Ta’addancin ‘Yan Bindiga

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bada shawarar wasu hanyoyi da za’a bi wajen magance matsalar ‘yan bindiga dake neman zama ruwan dare, inda ya bada shawarar cewa a rika gina makarantu kusa da sansanin sojoji domin kare harin yan bindiga a jihar.

Yayin da ya ke magana a shirin gidan talabijin na kasa, NTA, a ranar Juma’a, El-Rufai yace za a iya dakile harin idan sojoji za su iya isa makarantun cikin mintuna 30.

El-Rufai ya ce jihar na cigaba da aiki kan matakan dakile wasu hare-haren a gaba ciki har da ware kudade don gina katanga a makarantu. Ya kuma ce Kaduna na bukatar karin sojoji a wuraren da abubuwan ke faruwa domin kalubalen tsaron ya fi karfin yan sanda da jami’an tsaro na Civil Defence wato NSCDC.

Gwamnan ya zayyana matakai uku da jihar za ta dauka don dakile hare-haren na yan bindigan 1. Gina katanga a makarantu domin rashin katanga na saukaka wa bata gari yin kutse. 2. Samar da karin jami’an tsaro da suka hada da sojojin, Civil Defence, Masu tsaro na sirri, yan sa-kai da wadanda za su rika sa ido domin su sanar da hukuma idan sun ga an kawo hari. 3. Samar da sansanin sojoji kusa da makarantu ta yadda sojoji za su iya isa makarantun cikin minti 30.

El-Rufai ya ce binciken da suka yi ya nuna cewa yan bindigan sun fi kai hari makarantun kwana da ke kauyuka sannan da dare suke kai harin.

Labarai Makamanta