El Rufa’i Mutum Ne Mai Kunnen Ƙashi – Dr Arɗo

An bayyana Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru Ahmad El Rufa’i a matsayin wani mutum hutsu mai kunnen ƙashi wanda bai damu da halin da jama’ar Jihar shi suke ciki ba gaba ɗaya.

Wani mai fashin baƙi akan harkokin siyasar Najeriya Dr Umar Arɗo ne ya bayyana hakan a yayin tattaunawa da manema labarai da ya yi a kaduna a wajen taron karrama ɗaliban kwalejin koyon dabarun noma dake Afaka waɗanda aka ceto daga hannun ‘yan bindiga ƙarkashin jagorancin Sheikh Dr Ahmad Gumi.

Dr Arɗo ya ƙara da cewar taurin kai da kunnen ƙashi na Gwamna El Rufa’i shine silar jefa rayuwar jama’a musamman daliban manyan makarantu cikin hatsari na fargabar mamayar ‘yan Bindiga.

“Ya kamata El Rufa’i ya sani cewa wadannan dalibai da ‘yan bindiga suka sace ‘ya’ya ne na jihar Kaduna, suna da hakki a kashe ko nawa ne wajen ceto su daga hannun ‘yan bindiga, domin tabbas rai ya fi dukiya”.

Dr Arɗo ya yaba namijin kokarin da sanannen malami Dr Gumi ya yi na shiga gaba wajen ceto ɗaliban, sannan ya tabbatar da cewa shirye shirye sun yi nisa wajen ceto ɗaliban jami’ar Greenfield dake hannun ‘yan bindiga waɗanda El Rufa’i ya yi watsi da sha’anin su.

Dr Arɗo ya tabbatar da cewa sulhu da ‘yan bindiga shine mafita, kuma muddin aka bi wannan tafarki babu shakka za’a kai ga nasara.

Labarai Makamanta